logo

HAUSA

Ko ‘yan Najeriya za su yi watsi da babur a wata rana?

2021-10-14 19:33:33 CRI

Ko ‘yan Najeriya za su yi watsi da babur a wata rana?_fororder_20211014-sharhi-keke-Bello

Idan za ka tafi wani wuri, za ka je da babur ne, ko kuma da keke?

Har yanzu na kan tuna da yadda ake samun dimbin Okada dake gudu cikin sauri a titunan birnin Lagos. Watakila kashi 90% na jama’ar Najeriya za su zabi babur, saboda yana da sauri, zai iya kai ka wani wuri mai nisa, kana gwamnatin kasar Najeriya tana ba da kudin tallafi don rage farashin man fetur. Sai dai ya kamata mu tuna da cewa, hawan babur ba wata hanya ce da za ta dore ba, cikin hanyoyin zirga-zirga.

Mene ne ake nufi da kalmar “dorewa” a nan? Ma’anar wato zaman al’umma zai iya samun ci gaba mai dorewa, a fannonin muhallin halittu, da tattalin arziki, da dai sauransu. Amma me ya sa hawan babur ya kasance wata hanyar da ba za ta dore ba? Dalili shi ne, a wani bangare, makamashi na mai zai kare. Wani hasashen da aka yi a shekarar 2018 ya nuna cewa, za a iya ci gaba da haka da samar da danyen mai a kimanin wasu shekaru 50 a kasar Najeriya, kafin ya kare. Yayin da a daya bangaren kuma, yadda ake kone man fetur yana samar da hayaki mai guba da dumamar yanayi. Misali, birnin Lagos na cikin biranen da suka fi fama da matsalar gurbacewar iska a duniya, sakamakon yadda ake yawan yin amfani da injunan janaraito da motocin takunbo masu samar da hayaki da yawa. Saboda haka, raya fasahohin zirga-zirga masu dorewa ya wajaba ga Najeriya, da sauran kasashe daban daban.

A nata bangare, kasar Sin, bisa matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma, ita ma tana fuskantar bukatar kare muhallin halittu, da daidaita tsarin makamashi. Wannan ya sa kasar ta dauki dimbin matakai a shekarun nan don raya fasahohin zirga-zirga masu dorewa, tare da samun nagartaccen sakamako. Yanzu misali, a birnin Beijing da nake zama, an takaita yawan motocin da za su iya zirga-zirga kan tituna, amma duk da haka, motocin lantarki, da kekuna na lantarki (wadanda suke maye gurbin babur) na ta karuwa. Ban da wannan kuma, ana gudanar da bincike kan motoci masu aiki da mai a kai a kai, inda idan mota ta fara fitar da hayaki fiye da kima, to, za a umarci a gyara ta, ko kuma daina yin amfani da ita. Ta wannan hanya, yawan hayaki mai guba da motoci suka fitar a kasar Sin ya ragu da kashi 65.2%, daga shekarar 2012 zuwa ta 2019. Sa’an nan a fannin zirga-zirgar jama’a, misali motocin bas, da jiragen kasa, yawancinsu suna aiki da wutar lantarki. Kana ana yin amfani da fasahohin zamani wajen kula da aikin zirga-zirga: Yayin da nake shirin zuwa wani wuri, na kan yi amfani da wani APP din dake cikin wayar salula don duba yanayin zirga-zirga, sa’an nan zan bi ta wasu hanyoyi don magance gamuwa da cunkuson motoci, ko kuma zan shiga jirgin kasa dake tafiya a karkashin kasa, da hawan kekunan da ake ba da su haya, don magance dakatarwa a hanya, tare da samar da gudunmowa ga kare muhalli.

Na san idan an kwatanta da kare muhalli, abin da jama’ar Najeriya suka fi bukatar shi ne guraben aikin yi. Sai dai fasahohin da kasar Sin ta samu sun nuna cewa, za a iya raya tattalin arziki da kare muhalli a lokaci guda. Idan an dauki matakai masu dacewa, za a iya magance bin sawun wasu kasashen yamma wajen “ gurbata muhalli da farko, sa’an nan a fara daidaita shi”. Yanzu kasar Sin da kasar Najeriya suna hadin gwiwa da juna a karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da Sin ta gabatar, inda Sin ta taimakawa Najeriya wajen shimfida layin dogon da ya hada Abuja da Kaduna, da gina wani layin dogo na musamman a cikin birnin Abuja. Duk wadannan abubuwa sun kasance tushen raya fasahohin zirga-zirga masu dorewa. Nan gaba, bisa zurfafa hadin gwiwar Najeriya da Sin ta fuskar fasahohi, za a dinga samun ci gaba a wannan fanni. A lokacin da mutanen Najeriya za su iya tuka motoci da kekuna na lantarki, wadanda aka samar da su a Najeriya, suna gudu a kan hanyoyi na zamani, wadanda ba za su samu cunkuson motoci ba bisa wasu fasahohi na daidaita yanayin zirga-zirga, to, mutanen za su fadi a cikin zukatansu cewa, “ Wa zai bukaci babur?” (Bello Wang)