logo

HAUSA

An gano gawar mutane 25 da aka binne a manyan kaburbura a yankin Tarhuna na kasar Libya

2021-10-13 14:24:32 CRI

An gano gawar mutane 25 da aka binne a manyan kaburbura a yankin Tarhuna na kasar Libya_fororder_1013-Libya-Ahmad

Hukumomi a kasar Libya sun bayyana cewa, an gano gawarwakin wasu mutane 25 da ba a tantance su ba a cikin wasu sabbin manyan kaburbura da aka gano a birnin Tarhuna.

Yankin mai tazarar kilomita 90 daga babban birnin kasar Tripoli, Tarhuna ya taba zama babbar cibiyar rundunar sojojin kasar Libya masu sansani a gabashin kasar a lokacin da suke gwabza yaki da mayakan dakarun gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD a yankunan Tripoli da kewaye.

Kabari na farko na dauke da gawarwakin mutane 10, kabari na biyu na dauke da gawar mutane 9, na uku na dauke da mutane 4, yayin da ragowar kaburburan biyu na dauke da gawarwakin mutane biyu kowannensu, babbar hukumar gudanar da bincike da tantancewa ta kasar ta bayyana cewa, tana cigaba da aikin binciko karin wasu kaburbura a birnin.

A makon da ya gabata, an gano gawar mutane 10 cikin wasu manyan kaburbura biyu a Tarhuna. (Ahmad)