logo

HAUSA

Mu Gani A Kasa…

2021-10-13 18:39:30 cri

Mu Gani A Kasa…_fororder_2

A kwanakin baya ne Amurka ta yi alkawarin samar da tallafin alluran riga kafin cutar COVID-19 ga duniya ba tare da bata lokaci ba. Sai dai duk da cewa, wannan albishir ne mai dadin ji, amma jama’a na nuna shakku kan wannan furuci na Amurka, duba da cewa, wannan ba shi ne karon farko da Amurka ke irin wannan alkawari, amma sai maganar ta bi ruwa. Koma dai mene ne, mu gani a kasa, wai kare ya ce ana biki a gidansu. Rashin cika duk wani alkawari komai kankantansa, yana zubar da kimar kasa.

Wasu rahotanni na cewa, Amurka tana da babatun cewa, za ta samarwa duniya alluran da suka zarce wadanda sauran kasashe suka samar. Haka kuma ba kamar kasashen Sin da Rasha ba, wai Amurkar za ta samar da alluran ba tare da wani sharadi ba. Amma idan ka ga kare yana shinshina takalmi to dauka zai yi.

Kan wannan batu ne, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya ce, alluran riga kafi abu ne da ake amfani da shi wajen yaki da annoba da ceton rayuka, ma’ana bai dace a siyantar da shi ba.

Don haka, kasashen duniya ciki har da kasar Sin na fatan Amurka za ta gaggauta cika alkawarin da ta yi, maimakon maganar fatar baka, don samarwa duniya alluran riga kafi, musamman kasashe masu tasowa. Kyawun alkawari dai aka ce cikawa.

Masu fashin baki na cewa, kafin Amurka ta kai ga cika wannan alkawari, ya kamata ta hada kai da bangaren masanan MDD don ganin an gudanar da aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19 kamar yadda aka yi a kasar Sin, ta kuma daina boye riga kafin, matakin da zai sanya duniya ta fara aminta da abin da za ta iya fada game da aikin yaki da wannan annoba.

Sannin kowa ne cewa, ya zuwa yanzu kasar Sin ta samar da alluran riga kafin COVID-19 biliyan 1.2 ga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 100, da kuma kayayyakin yaki da cutar ga sama da kasashe 150 da kungiyoyin kasa da kasa 14, ba kuma tare da gindaya wani sharadi ko siyasantar da wannan batu ba. Yanzu dai duniya na jiran ganin ko dai a wannan karon da gaske Amurka za ta cika alkawarin da ta yi. Domin ba a yabon Dan-kuturu, sai an ga ya shekara da yatsa. (Ibrahim Yaya)