logo

HAUSA

Firaministar kasar Tunisiya ta kafa sauwar gwamnati

2021-10-12 15:46:45 CRI

Firaministar kasar Tunisiya ta kafa sauwar gwamnati_fororder_src=http___news.cnhubei.com_a_10001_202110_4ae53ed51937706d91d2af52ed64c5d7.jpeg&refer=http___news.cnhubei

Firaministar kasar Tunisiya Najla Bouden Romdhane ta nada sabbin ministocin gwamnatin kasar a jiya Litinin, inda shugaban kasar Kais Saied ya rantsar da ita.

Sabuwar gwamnatin Najla Bouden Romdhane ta kushi ministoci 24 da sakandare mai kula da harkokin waje, ciki har da mata 9.

Najla Bouden Romdhane ta shedawa manema labarai a wannan rana cewa, aikin dake gaban sabuwar gwamnatin, shi ne sake samun amincewa daga jama’ar kasar da hukumomin kasashen waje, musamman ma mai da hankali kan yaki da cin hanci da karbar rashawa, da kyautata zaman rayuwar jama’a da daga karfin gwamnati wajen aiwatar da harkokin kasar, da ingiza farfadowar tattalin arzikin kasar da warware matsalar samar da guraben aikin yi ga matasa da kuma samar da hidimma mai inganci ga al’umma.

An nada Najla Bouden Romdhane a matsayin sabuwar firaministar kasar a ran 29 ga watan Satumba, ita ce mace ta farko da ta zama firaminista a tarihin kasar. (Amina Xu)