logo

HAUSA

Bangarorin dake yaki da juna a Libya sun amince su janye dakarunsu da mayakan kasashen waje

2021-10-11 11:05:59 CRI

Bangarorin dake yaki da juna a Libya sun amince su janye dakarunsu da mayakan kasashen waje_fororder_1011-Libya-Ahmad

Tawagar aikin wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar Libya ta sanar a ranar 10 ga wata cewa, sabon zagayen tattaunawar sulhun da aka gudanar a birnin Geneva na kasar Switzerland, tsakanin wakilan dukkan bangarorin dake yaki da juna a Libya, ta haifar da muhimmin sakamako. Tun da farko bangarorin biyu sun cimma matsayar za su janye dakarunsu da kuma na kasashen waje.

Rahotanni sun bayyana cewa, wani kwamitin sojoji na hadin gwiwa wanda ya kunshi wakilai biyar-biyar daga dukkan bangarorin dake yaki da juna a Libya sun kammala taron tattaunawa na tsawon kwanaki uku a  Geneva. Bangarorin biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniya da nufin baiwa mayakansu da dakarun kasashen waje damar ficewa daga kasar Libyan sannu a hankali, kana bisa tsari yadda ya kamata. Wakilan sun bayyana cewa, bayan sun koma Libya, za su tattauna da kasashen da abin ya shafa game da yadda za su taimaka wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka tsara domin mutunta ikon da kasar Libya ke da shi kan yankunanta.

Jami’an MDD da abin ya shafa sun bayyana cewa, ya kamata dukkan bangarorin da ba sa ga maciji da juna a Libya su yi amfani da irin nasarorin da aka cimma a baya bayan nan domin dorawa zuwa mataki na gaba, kana a yi kokarin kafa sabuwar gwamnati wacce za ta samu amincewar dukkan bangarorin kasar ta hanyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe a kasar. (Ahmad)