logo

HAUSA

Kasashen EAC sun yi hasarar kashi 92 na kudin shiga a yawon shakawa saboda COVID-19

2021-10-11 10:47:25 CRI

Kasashen EAC sun yi hasarar kashi 92 na kudin shiga a yawon shakawa saboda COVID-19_fororder_1011-EAC-Ahmad-yawon bude ido

Kasashe shida na mambobin kungiyar kasashen gabashin Afrika EAC, sun tafka hasarar kashi 92% na kudaden shigarsu daga fannin yawon bude ido sakamakon barkewar annobar COVID-19, kamar yadda babban sakataren EAC Peter Mathuki ya bayyana.

A wata sanarwa da aka fitar a daren Asabar, Mathuki ya bayyana cewa, yawan masu zuwa yawon shakatawa a shiyyar ya ragu daga mutane miliyan 6.98 gabanin barkewar annobar zuwa mutane miliyan 2.25 a halin yanzu, lamarin ya haifar da hasara, ya kara da cewa, fannin yawon bude ido shi ne ya fi fuskantar mummunar koma baya a sakamakon annobar.

Mathuki ya ce, a halin yanzu an sake bude harkokin kasuwancin, inda ya bukaci gwamnatocin mambobin kasashen EAC da sauran masu ruwa da tsaki da su yi aiki tare domin janyo hankalin masu sha’awar yawon bude ido zuwa shiyyar da kuma masu sha’awar sayen kayayyaki, a matsayin wani muhimmin kokari don tabbatar da gaggauta farfadowa fannin. Mambobin kasashen EAC su ne Burundi, Kenya, Rwanda, Tanzania, Sudan ta kudu da Uganda.

Duk da irin yadda annobar ta haifar da koma baya wajen samun kudade daga fannin yawon bude ido, jami’in ya ce suna da kwarin gwiwa cewa ta hanyar yin kokari tare, za su iya samun nasarar farfadowar al’amurra su koma yadda suke gabanin barkewar annobar ko ma fiye da hakan cikin kankanin lokacin da ya gaza shekaru biyar, Mathuki, ya bayyana hakan ne a wajen bikin baje kolin yawon bude ido na farko na shiyyar gabashin Afrika wanda aka gudanar a birnin Arusha dake arewacin kasar Tanzania, inda kuma can ne helkwatar kungiyar ta EAC. (Ahmad)