logo

HAUSA

Sudan ta kudu ta amince da fitar da dala miliyan 100 domin biyan bashin da ake bin ofisoshinta dake ketare

2021-10-11 10:34:40 CRI

Sudan ta kudu ta amince da fitar da dala miliyan 100 domin biyan bashin da ake bin ofisoshinta dake ketare_fororder_1011-S.Sudan-Faeza

Gwamnatin riko na kasar Sudan ta Kudu, ta amince da fitar da dala miliyan 100 domin biyan bashin da ake bin ofisoshinta dake ketare, tun daga shekarar 2015 da ta yanke shawarar rufe su.

A cewar Micheal Makuei Lueth, ministan yada labarai na kasar, an umarci ma’aikatar kudi ta kasar ta fitar da kudi domin biyan bashin, yana mai cewa tun daga wancan lokaci, kasar ke rasa matsayinta na mamba a wasu hukumomin kasa da kasa.

Ministan ya ce wasu daga cikin ofisoshin kasar dake hukumomin kasa da kasa da na jakadanci, na fuskantar matsalar kudi, inda wasu suka rufe. Yana mai cewa suna rasa matsayinsu na mamba a wasu hukumomin shiyya ko na duniya, kawai saboda kasar ba ta biya kudin da ya kamata ta biya a matsayinta na mamba ba.

Bisa tilas a shekarar 2015, kasar ta rage yawan jami’an diflomasiyyarta saboda matsalar kudin da ta samo asali daga rikicin da aka shafe sama da shekaru 6 ana yi tun 2013.  (Fa’iza Mustapha)