logo

HAUSA

An karrama shugabar Tanzania saboda yadda take inganta bangaren yawon bude ido

2021-10-10 16:36:27 CRI

An karrama shugabar Tanzania saboda yadda take inganta bangaren yawon bude ido_fororder_微信图片_20211010163608

Majalisar kula da yawon bude ido ta Afrika ATB, ta karrama shugabar kasar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, saboda gagarumar gudunmuwar da take ba bangaren yawon bude ido na kasarta.

A jawabin bude taron baje kolin harkokin yawon bude ido na kungiyar raya yankin gabashin Afrika a birnin Arusha dake arewacin kasar Tanzania, Cuthbert Ncube, shugaban majalisar ATB, ya ce shugabar Tanzania na kokarin tabbatar da farfadowar bangaren yawon bude ido na kasar, yayin da ake fama da annobar COVID-19.

Tanzania ce kasa ta farko daga yankin gabashin Afrika da ta karbi bakuncin baje kolin bangaren yawon bude ido na yankin, wanda aka fara daga jiya Asabar zuwa gobe Litinin, 11 ga wata.

Baje kolin na da nufin wayar da kai game da damarmakin zuba jari a bangaren yawon bude ido da tallata yankin gabashin Afrika a matsayin wurin yawon bude ido yayin da ake fama da COVID-19. (Fa’iza Mustapha)