logo

HAUSA

An kashe mayakan BH 2 da farar hula 1 a yankin arewa mai nisa na Kamaru

2021-10-10 16:25:42 CRI

Akalla mayakan BH biyu aka kashe tare da wani farar hula, a samamen da jami’an tsaro suka kai yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru.

Wani jami’in soji da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, dakarun gwamnati sun yi wa mayakan kungiyar BH kwantar bauna, lamarin da ya yi sanadin mutuwar 2 daga cikinsu, jiya Asabar a yankin Mozogo.

A cewar wani ganau, da farko a daren ranar Juma’a, mayakan BH sun kai hari kauyen, inda suka kashe mutum guda tare da lalata kadarori.

Samamen na dakarun gwamnati ya zo ne kwanaki 3 bayan mayakan sun farwa kauyen Assighassia dake yankin, inda suka kashe fararen hula 7.

Kafofin watsa labarai na kasar sun ruwaito cewa, mayakan sun kaddamar da hare-haren ne bayan jami’an tsaro sun kai hari maboyarsu, lamarin da ya kai ga kisan ‘yan ta’addan da dama. (Fa’iza Mustapha)