logo

HAUSA

Hukumar kare hakkin dan adam ta MDD ta zartas da kuduri kan batutuwan dake shafar mulkin mallaka

2021-10-09 16:15:31 CRI

Jiya Juma’a 8 ga wata, an kira taron hukumar kare hakkin dan adam ta MDD karo na 48, inda aka zartas da kuduri mai taken “mummunan tasirin da batutuwan da ba a warware ba sakamakon mulkin mallaka ke kawowa aikin kare hakkin dan adam” wanda kasar Sin ta gabatar, kudurin ya yi nuni da cewa, batutuwan da ba a warware su ba sakamakon gudanar da mulkin mallaka, kamar su rage albashin da ake biyan ma’aikata, da rashin daidaito tsakanin sassa daban daban a cikin kasa ko tsakanin kasa da kasa, da nuna kabilanci, da take hakkin al’ummun kasa, wadanda suka rayu a kasar tun tuni, da lalata al’adun gargajiya da sauransu, duk suna kawo mummunan tasiri ga hakkin dan adam, don haka yana da muhimmanci a kawar da duk wadannan matsalolin domin tabbatar da kare hakkin dan adam yadda ya kamata.

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Chen Xu, ya bayyana cewa, yanzu haka matsalolin suna ci gaba da gurgunta hakkin dan adam da zaman lafiya da ci gaban duniya, wajibi ne hukumar kare hakkin dan adam ta MDD ta kara maida hankali kan batun kuma ta shirya tattaunawa kan batun.(Jamila)