logo

HAUSA

Yang Jiechi ya gana da mashawarcin Amurka a fannin tsaron kasa

2021-10-07 15:24:00 CRI

Yang Jiechi ya gana da mashawarcin Amurka a fannin tsaron kasa_fororder_yang jiechi

Mamba a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS Yang Jiechi, ya gana da mai baiwa gwamnatin Amurka shawara kan harkokin tsaron kasa Jake Sullivan, a jiya Laraba a birnin Zurich na kasar Switzerland.

Yayin zantawar manyan jami’an, sun zurfafa shawarwari da musaya, game da alakar kasashen biyu, tare da tattauna ra’ayoyi kan batutuwan da suka shafi kasa da kasa, da na shiyyoyi dake jan hankalin kasashen.

Ana kallon wannan ganawa dai a matsayin wadda ke cika da nasara, wadda kuma za ta taimaka wajen kara inganta fahimtar juna da aminci tsakanin Sin da Amurka.

Sassan biyu sun amince da aiwatar da wasu matakai, bisa tattaunawar da shugabannin kasashen biyu suka gudanar ta wayar tarho a ranar 10 ga watan Satumban da ya shude, tare da karfafa muhimman tattaunawa, da warware sabani yadda ya kamata, da kaucewa fito na fito. Kaza lika sun amince su kara azama wajen zakulo hanyoyin da kasashen biyu za su ci gajiya daga juna, tare da yin aiki tare, wajen sake dawo da alakar Sin da Amurka kan turba mai inganci, tare da ciyar da ita gaba.

Cikin kalaman sa yayin tattaunawar, Yang ya ce ikon sassan biyu na cimma nasarar kyautata alakar su, zai shafi nasarar manufofin bunkasa kasashen da al’ummun su, da ma moriyar sauran sassan duniya baki daya.  (Saminu)