logo

HAUSA

Tanzania ta karbi taragon dakon kaya kirar kasar Sin

2021-10-07 16:06:58 CRI

Tanzania ta karbi taragon dakon kaya kirar kasar Sin_fororder_tanzaniya

A jiya Laraba ne hukumar dake lura da layin dogo ta kasar Tanzania, ta sanar da karbar wasu sabbin taragon dakon kaya kirar kasar Sin guda 44, karkashin wani tallafin bunkasa aiki da layin dogo na kasar, wanda bankin duniya ya samar da kudin gudanarwa.

Babban daraktan hukumar ta TRC a Tanzania Masanja Kadogosa, ya ce ko wane tarago na iya daukar kayan da suka kai tan 46. Za kuma a rika amfani da su wajen dakon hajoji tsakanin tashar jiragen ruwa ta birnin Dar es Salaam zuwa yammaci da arewacin kasar.

A hannu guda kuma, sabbin taragon dakon kayan za su taimaka wajen safarar kayayyaki tsakanin Tanzania da kasashen Uganda da Rwanda, da Burundi da janhuriyar dimokaradiyyar Congo, da ba su da iyaka da teku.  (Saminu)