logo

HAUSA

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD ya bukace kasashen da abin ya shafa su daidaita kura kuransu kan batun ETIM

2021-10-07 15:51:24 CRI

A ranar 6 ga watan Oktoba, kwamitin dokoki na babban taron MDD karo na 76 ya gabatar da mahawara mai taken “Matakan kawar da ayyukan ta’addanci na kasa da kasa." A cikin jawabinsa, Geng Shuang, mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD, ya soki daidaikun kasashe bisa matakin da suka dauka na tsame kungiyar fafutukar musulunci ta gabashin Turkestan ko kuma (ETIM) daga cikin jerin sunayen kungiyoyin ‘yan ta’adda dake hannunsu, inda ya soke su bisa ba da uzuri da kuma nuna fifiko, kana ya bukaci kasashen da abin ya shafa da su dauki matakai bisa tsarin kasa da kasa. Idan aka fara tun daga matakin yanayin hadin gwiwar yaki da ayyukan ta’addanci, sai kuma a gaggauta gyara kura kuran da aka aikata, kana a ayyana kungiyar ETIM a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

Geng Shuang ya bayyana cewa, ETIM kungiyar ta’addanci ta kasa da kasa ce wadda kwamitin sulhun MDD ya sanya ta, kawar da kungiyar ta’addanci ta ETIM wani muhimmin aiki ne na yaki da ta’addanci na kasa da kasa, kuma ya dace da bukatun al’ummun kasa da kasa. Rahoton tawagar kwararru da kwamitin sulhun MDD ya kafa ya nuna cewa, kungiyar ETIM har yanzu tana da karfi. Kungiyar tana da dubban mayaka a kasar Syria da kuma wasu daruruwan mambobi a kasar Afghanistan. Har yanzu tana ci gaba da tuntubar sauran kungiyoyin ta’addanci kuma tana ci gaba da shirye shiryen horar da mambobinta domin shirya ayyukan ta’addanci. Ana ci gaba sakin sakonni a kai a kai na muryoyi da bidiyoyi na shirye shiryen kaddamar da ayyukan ta’addanci na kungiyar.

Geng Shuang ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan dukkan bangarorin da abin ya shafa za su duba batun mummunan hadarin dake tattare da ta’addancin kungiyar ETIM, kana su fahimci irin kokarin da kasar Sin ke yi wajen yaki da ayyukan ta’addanci.(Ahmad)