logo

HAUSA

Kasar Sin tana sahun gaba wajen shigo da kofi daga Habasha

2021-10-07 16:25:00 CRI

Kasar Sin tana sahun gaba wajen shigo da kofi daga Habasha_fororder_kofi

Hukumar kula da kofi da ganyen shayi ta kasar Habasha ta sanar cewa, har yanzu kasar Sin tana sahun gaba cikin jerin kasashen dake shigo da kofi daga kasar Habasha, ya zuwa watan Agustan wannan shekara.

A bisa shirin da kasar ta yi na samar da kudi dalar Amurka miliyan 99.38 ta hanyar fitar da ton 29,819.74 na kofi da kayan yaji zuwa ketare a kowane wata, kasar Habashan ta samu kudin da ya kai dala miliyan 125.82 ta hanyar fitar da ton 33,169.45 na hajojinta, inda kasar ta samu bunkasuwa ta fuskar yawan kayayykin da ta fitar da ma kudaden shigarta, kamar yadda hukumar ta bayyanawa manema labarai.(Ahmad)