logo

HAUSA

An aike da jami’an wanzar da zaman lafiya garin Matchika na CAR bayan aukuwar mummunan hari

2021-10-07 15:57:23 CRI

Kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric, ya ce an aike da  rukunin jami’an wanzar da zaman lafiya zuwa garin Matchika na janhuriyar Afirka ta tsakiya wato CAR , bayan aukuwar wani mummunan hari da ya haifar da asarar rayuka.

Mr Dujarric, ya ce jami’an da aka aike Matchika, suna tattara bayanai game da halin da ake ciki, tare da tabbatar da kare rayukan fararen hula. Kawo yanzu dai ba a kai ga tantance adadin fararen hula da suka rasu, ko suka jikkata a tashin hankalin ba.  (Saminu)