logo

HAUSA

Jakadan Sin ya bukaci a tattauna batun korar da Habasha ta yiwa jami’an MDD

2021-10-07 16:10:57 CRI

Wakilin kasar Sin ya bukaci MDD da gwamnatin kasar Habasha da su warware takaddamar batun sallamar ma’aikatan MDD bakwai daga kasar.

Zhang Jun, wakilin dindindin na kasar Sin a kwamitin sulhun MDD, ya bayyanawa taron kwamitin sulhun kan batun kasar Habasha cewa, babban abin da ya kamata a baiwa fifiko a yanzu shi ne a dauki hakikanin matakan diflomasiyya domin kaucewa tabarbarewar al’amurra.

Ya kara da cewa, suna karfafawa dukkan bangarorin gwiwa da su ci gaba da tuntubar juna, da yin musayar bayanai, kana su yi aiki tare don samun maslaha, sannan a guji lalata amincin da ake da shi da kuma hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu.

A ranar 30 ga watan Satumba gwamnatin kasar Habasha ta sanar da korar ma’aikatan MDD bakwai daga kasarta bisa abin da ta kira cewa suna yi mata shisshigi a harkokin cikin gidan kasar, inda ta ba su wa’adin sa’o’i 72 da su fice daga kasar ta Habasha.(Ahmad)