logo

HAUSA

ECOWAS ta fara aikin sake fasalin tsarin samar da hidima mai inganci

2021-10-06 15:14:03 CRI

Jiya ne shugabannin kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) suka fara yin garambawul ga kungiyar, a wani mataki na samar da ingantaccen hidima don amfanar dukkan 'yan kasa dake yankin.

Shugabar majalisar ministocin ECOWAS Shirley Ayorkor Botchway, ta bayyana cewa sake fasalin, a matsayin wani bangare na manyan sauye sauye, zai rage yawan kwamishinoni daga 15 zuwa 7.

A jawabinta na budewa a wani zama na musamman na majalisar ministocin, Botchway ta ce manufar sake fasalin, ita ce kirkiro tsarin gudanarwa da zai bukaci karin kudade.

Botchway, wadda har ila ita ce ministar harkokin wajen Ghana ta ce, babban makasudin mu shi ne samar da ingantacciyar cibiyar ECOWAS wadda za ta samar da ingantaccen hidima ga mutanen mu.(Ibrahim)