logo

HAUSA

Sabon jami’in Mintel: Ya dace kamfanonin duniya su mai da hankali kan kasar Sin

2021-10-06 15:41:35 CRI

Sabon babban jami'in kamfanin Mintel na Burtaniya dake bincike kan harkokin kasuwa Matthew Nelson, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a cikin wata hira da aka yi da shi a kwanan nan cewa, abubuwa da yawa za su ci gaba da haifar da habakar kasuwar kasar Sin da samfuran duniya, don haka ya dace su mai da hankali kan kasar Sin.

Nelson ya ce, yana da kyakkyawan fata game da ci gaban kasuwar kasar Sin, kuma da gaske kasar Sin ita ce babbar kasuwa da ta bunkasa a shekarar 2020 wadda kuma ta yi nasarar dakile cutar COVID-19 a farkon shekarar da ta gabata, wannan na nufin cewa, tattalin arzikin kasar Sin bai girgiza ba, kuma zai ci gaba da habaka.

Nelson ya ce, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun ci gaba a shekarar 2021, an kuma dora shi a kan dabaru na dogaro da kai na fasaha, tare da daga matsayin rayuwa, da zaman takewar jama'a, da kuma tattalin arzikin maras gurbata muhalli. (Ibrahim)