logo

HAUSA

Afirka na koyon dabarun yaki da kwararowar hamada daga kasar Sin

2021-10-06 14:58:23 CRI

Masanan kasar Habasha sun bayyana cewa, kwarewar da kasar Sin ta samu wajen yakar kwararar hamada, ya samar da damammaki masu yawa ga Afirka, wanda ke bukatar dakile karuwar bala'in hamadar Sahara.

Kwanan nan hukumar abinci da aikin noma ta MDD (FAO) ta yi kiyasin cewa, nan da shekarar 2030, Afirka za ta yi hasarar kashi biyu bisa uku na filayenta idan ba a dakatar da kwararowar hamada cikin lokaci ba.

Masanin gandun daji na kasar Habasha, Adefris Worku ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua a wata hira da aka yi da shi kwanan nan cewa, wajibi ne kasashen Afirka su aiwatar da dabarun yaki da kwararowar hamada, ganin yadda matsalar kwararowar hamada ke zama ruwan dare, musamman a yankin kudu da hamadar Sahara.

Ya ce, irin nasarorin da kasar Sin ta samu wajen maido da filayen da ta rasa a baya, na zama wani bangare na manyan ayyukan da take yi na tallafa wa kasashen Afirka, don cimma burin da ake da shi a fannin gandun daji.

A cewar masanin, Afirka na iya koyo daga kasar ta Sin, tun daga inganta makamashi mai tsafta, samar da kudade a fannin sauyin yanayi, raba fasahohi, da ilimi da ayyukan maido da yanayin filaye.(Ibrahim)