logo

HAUSA

Jakadan Sin ya yi kira ga kasashen duniya da su kara azama wajen yaki da talauci da kare hakkokin bil adama

2021-10-06 15:33:04 CRI

Jakadan Sin ya yi kira ga kasashen duniya da su kara azama wajen yaki da talauci da kare hakkokin bil adama_fororder_chen xu

Jakadan dindindin na kasar Sin a ofishin MDD dake birnin Geneva Chen Xu, ya yi kira ga kasashen duniya da su zurfafa matakan dakile talauci, tare da samar da dabarun rage yaduwarsa, gwargwadon yanayin da kasashen su ke ciki.

Chen Xu ya yi wannan kira a yayin da yake jawabi a wani zama, a gefen taron hukumar kare hakkokin bil adama ta MDD karo na 48 dake gudana yanzu haka, inda ya ce daukar wadannan matakai, zai haifar da ci gaba bisa daidaito tsakanin al’umma.

Jakadan ya kara da cewa, akwai bukatar sassan kasa da kasa su zurfafa hadin gwiwa wajen yaki da talauci, da samar da tallafi ga kasashe masu tasowa. Kaza lika a cewarsa, ya kamata hukumomin kasa da kasa, kamar hukumar kare hakkokin bil adama ta MDD, su taka rawar gani wajen yakar fatara.

Chen Xu ya yi tsokacin ne yayin taro mai taken "Tasirin kawar da talauci a fannin bunkasawa da kare hakkokin bil adama", taron da ofishin wakilcin dindindin na kasar Sin a birnin Geneva, da hadin gwiwar tawagar nahiyar Afirka suka jagoranta. (Saminu)