logo

HAUSA

Mataimakin jakadan Sin a MDD ya yi kira da a maida hankali ga bukatun DRC

2021-10-06 15:47:56 CRI

Mataimakin jakadan dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga kwamitin tsaron majalissa, da ya nazarci damuwar da mahukuntan janhuriyar dimokaradiyyar Congo ke nunawa, don gane da takunkumai da aka kakabawa kasar.

Dai Bing, wanda ya yi tsokacin yayin zaman kwamitin tsaron MDD da aka shirya game da janhuriyar dimokaradiyyar Congo a jiya Talata, ya ce kamata ya yi kwamitin tsaron ya duba bukatar kasar, mai nasaba da sake daidaita takunkuman da aka sanya mata, domin kaucewa mummunan tasirin su a fannin inganta tsaro.

Dai ya kuma yabawa gwamnatin janhuriyar dimokaradiyyar Congo, bisa kwazonta na tsara shiri na shekaru 3, wanda zai maida hankali ga tabbatar da dawo da zaman lafiya, da wanzar da ci gaba mai dorewa a kasar.  (Saminu)