logo

HAUSA

Bai kamata wasu tsirarun kasashe su tsara yadda demokradiyya za ta kasance ba

2021-10-05 15:28:50 CRI

Zaunannen jakadan kasar Sin a MDD Chen Xu, ya jaddada cewa, babu wani tsari takamaimai dake bayyana ainihin demokradiyya, yana mai cewa, bai kamata wasu tsirarun kasashe su zama masu tsara yadda demokradiyyar za ta kasance ba.

Da yake jawabi a madadin rukunin wasu kasashe, Chen Xu ya bayyanawa taro na 48 na majalisar kare hakkin dan Adam, a ofishin MDD na Geneva cewa, zaman lafiya da ci gaba da daidaito da adalci da demokradiyya da ‘yanci, ka’idoji ne na bai daya na bil adama.

Ya nanata cewa, jigon demokradiyya na ainihi shi ne tantance ko ya dace da yanayin kasa, ko yana wakiltar muradun jama’a da kare bukatunsu da goya musu baya, kuma ko zai kawo zaman lafiya a fannin siyasa da ci gaban al’umma da zamantakewarsu.

A cewarsa, sun damu da fuska biyu da ake nuna kan batun demokradiyya, inda wasu ke amfani da ita wajen kakabawa wasu akidu da tsurukansu na siyasa.

Bugu da kari, jakadan ya ce fakewa da demokradiyya wajen tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen da iyakance ci gabansu, ya saba da demokradiyya, kuma zai haifar da rikici da tashin hankali, da tarnaki ga mutanen da batun ya shafa a fadin duniya. (Fa’iza Mustapha)