logo

HAUSA

Gwamnonin yankin Tafkin Chadi na tattaunawa domin inganta kwanciyar hankalin yankin

2021-10-05 16:19:56 CRI

An bude taro karo na 3 na gwamnonin yankin Tafkin Chadi a jiya Litinin, wanda ke da nufin inganta kwanciyar hankalin yankin.

Gwamnoni jihohi 8, daga yankunan da kungiyar BH ta addaba a kasashen Nijeriya da Niger da Chadi da Kamaru ne ke halartar taron dake gudana a birnin Yaounde na Kamaru.

Manufar taron ita ce, tantance ayyukan jin kai da yanayin tsaro a yankin, da ci gaban da aka samu wajen aiwatar da shirye-shiryen tabbatar da tsaro da gudunmuwar kungiyoyin al’umma wajen tabbatar da kwanciyar hankali a yankin.

Haka zalika, yayin taron, za a nazarci yanayin hadin gwiwa tsakanin fararen hula da soji da masu ayyukan agaji da nazartar damarmaki da kalubalen hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa da tantance damarmaki da mafita da dama da ake da su, na sake tsugunarwa da shigar da mutanen da a baya ke da alaka da kungiyar BH cikin al’umma. (Fa’iza Mustapha)