logo

HAUSA

Kasar Sin ta taimakawa Guinea-Bissau da kashi na biyu na sabbin alluran rigakafin COVID-19

2021-10-05 15:34:58 CRI

Kasar Sin ta taimakawa Guinea-Bissau da kashi na biyu na sabbin alluran rigakafin COVID-19_fororder_allura

A jiya ne, agogon wurin aka gudanar da bikin mika kashi na biyu na alluran rigakafin COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta baiwa gwamnatin Guinea-Bissau, bikin da ya gudana a Bissau, babban birnin kasar, kamar yadda ofishin babban kwamishinan yaki da annobar COVID-19 na kasar ya sanar.

Babban kwamishinan yaki da annobar COVID-19 na Guinea-Bissau ya bayyana cewa, tun bayan samun 'yancin kan kasar Guinea-Bissau, kasar Sin ta dade tana goyon bayan bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar ta Guinea-Bissau, tare da ba ta taimako mai yawa. Kuma al’ummar Guinea-Bissau ba za su taba mantawa ba. (Ibrahim)