logo

HAUSA

Kashin farko na rigakafin kasar Sin da Angola ta saya sun isa Luanda

2021-10-05 15:41:55 CRI

Kashin farko na rigakafin kasar Sin da Angola ta saya sun isa Luanda_fororder_angola

Kashin farko na alluran rigakafin COVID-19 miliyan 3 da Angola ta saya daga kasar Sin, sun isa Luanda, babban birnin kasar a jiya Litinin.

Jami’in gwamnatin Angola da ya karbi rigakafin, ya ce kasar Sin ta taimakawa kasarsa a yakin da take yi da annobar COVID-19 ta hanyar taimakon kayayyaki da musayar bayanai da fasahohi, kuma Angola na matukar yaba mata.

Ya ce gwamnatin Angola na bayar da muhimmanci ga aikin ba da rigakafin, kuma ta sayi allurai miliyan 10 daga kamfanonin kasar Sin. Ya kara da cewa, yanzu haka, Angola na tsaka da fama da barkewar cutar a zagaye na 3, don haka akwai bukatar gaggauta aikin bayar da rigakafin.

Kashin farko na allurai miliyan 3 da suka isa Luanda, za su taimaka wajen gaggauta aikin bayar da rigakafin, da komawa bakin aiki da harkokin zamantakewa a Angola. (Fa’iza Mustapha)