logo

HAUSA

Sin da kasashe masu ra'ayi daya sun nuna damuwa kan yadda ake nuna wariyar launin fata a wasu kasashe

2021-10-05 15:18:19 CRI

Sin da kasashe masu ra'ayi daya sun nuna damuwa kan yadda ake nuna wariyar launin fata a wasu kasashe_fororder_chen xu

Jiya ne kasar Sin da wasu gungun kasashe suka nuna matukar damuwarsu, kan yadda tsarin wariyar launin fata, da karuwar manyan laifukan nuna kiyayya ke samun gindin zama a wasu kasashe.

Da yake gabatar da sanarwar hadin gwiwa a madadin kasashe masu irin wannan ra'ayi a yayin taron hukumar kare hakkin dan Adam na MDD karo na 48, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva Chen Xu, ya lura cewa, a bana ne yarjejeniya da shirin aiki na Durban(DDPA) ke cika shekaru 20 da kafuwa.

A cewar ofishin kare hakkin dan Adam na MDD, DDPA wani cikakken bayani ne kuma mai hangen nesa, wanda ya kunshi kudurin kasa da kasa na magance matsalar nuna wariyar launin fata ta kowane fanni da yadda take bayyana.

Sanarwar hadin gwiwar ta bayyana cewa, duk da cewa an amince da namijin kokarin da kasashen duniya suka yi na yaki da wariyar launin fata, har yanzu akwai sauran tafiya wajen kawar da nuna wariyar launin fata, da kyamar baki da rashin jituwa da suka danganci juna.(Ibrahim)