logo

HAUSA

Yawan wadanda suka mutu sakamakon bam din da ya fashe a wani masallaci a Afghanistan ya karu zuwa 8

2021-10-04 15:34:46 CRI

Yawan wadanda suka mutu sakamakon bam din da ya fashe a wani masallaci a Afghanistan ya karu zuwa 8_fororder_00

Rahotannmi daga kasar Afghanistan na cewa, adadin wadanda suka mutu sakamakon fashewar wani bam a wajen wani babban masallaci a Kabul, babban birnin Afghanistan, ya karu zuwa 8, yayin da wasu mutane 20 suka jikkata.

Fashewar ta faru ne a tsakiyar jama'a a kofar babban masallacin Eidgah jiya Lahadi, lokacin da ake gudanar da taron addu'ar mahaifiyar kakakin Taliban Zabihullah Mujahid da Allah ya yiwa rasuwa.

Haka kuma, Mujahid yana aiki a matsayin mataimakin ministan watsa labarai da al'adu a gwamnatin rikon kwarya ta Taliban.

Rahotannin farko sun ce, fararen hula biyu sun mutu, yayin da wasu hudu suka jikkata a lamarin. Rahoton ya ce sojojin Taliban sun cafke mutane uku da ake zargi a kusa da masallacin.

Kawo yanzu dai, babu wata kungiya da ta dauki alhakin fashewar bam din.

Yanayin tsaro ya dan daidaita a fadin Afghanistan, tun lokacin da Taliban ta karbi iko a tsakiyar watan Agusta.

Sai dai kuma, ana samun hare-haren bama-bamai wadanda mayakan da ke da alaka da kungiyar IS suka kaddamar a Kabul, da birnin Jalalabad, babban birnin lardin Nangarhar na gabashin kasar, a cikin makwannin da suka gabata.(Ibrahim)