logo

HAUSA

‘Yan sanda sun kashe ‘yan bidiga 5 a arewa maso yammacin Nijeriya

2021-10-03 16:10:01 CMG

‘Yan sanda sun kashe ‘yan bidiga 5 a arewa maso yammacin Nijeriya_fororder_3

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da kisan ‘yan bidinga 5 yayin wani samame da jami’anta suka kai maboyarsu dake jihar Zamfara na arewa maso yammacin kasar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara Ayuba Elkanah, ya shaidawa manema labarai a Gusau babban birnin jihar cewa, an kuma kama wasu da ake zargi da suka hada da shugaban ‘yan bindigar tare da wasu mutane 21, yayin samamen da ‘yan sanda suka kai yankin karamar hukumar Gumi a ranar Juma’ar da ta gabata.

Kwamishinan ya ce, samamen da aka kai yanki Gumi, ya biyo bayan bayanan sirri da suka samu da wani samame da aka kai dajin Kagara dake yankin. 

Ya kara da cewa, shugaban ‘yan bindigar mai suna Bello Rugga, shi ne ke jagorantar ayyukan bata garin a dajin Kagara da yankunan dake kewaye da baki dayan yankin karamar hukumar Gumi.

Haka kuma, shi ne ke shirya jerin hare-haren dake kai wa ga kisan mutanen da basu-ji-basu-gani-ba, tare da sace wasu mutanen da dama domin neman kudin fansa. (Fa’iza Mustapha)

Faeza