logo

HAUSA

Kasashen duniya 75 har da kasar Sin sun yi kira a tabbatar da daidaito a rabon rigakafi

2021-10-02 15:33:15 CRI

Kasashen duniya 75 har da kasar Sin sun yi kira a tabbatar da daidaito a rabon rigakafi_fororder_allura

Wasu kasashen duniya 75, ciki har da kasar Sin, sun yi kiran a tabbatar da hadin kai da kuma adalci a tsarin rabon rigakafi a yayin da kwamiti na uku ya tafka muhawara a taron kolin MDD.

A sanarwar hadin gwiwa da kasashen suka fitar, sun bayyana cewa, annoba babu ruwanta da kan iyakoki. Matakin da za a dauka ya dogara ne kan hadin gwiwar kasa da kasa, da hada kai da hadin gwiwar bangarori daban daban.

Sanarwar wanda wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun ya karanta, an bukaci dukkan kasashen duniya da masu ruwa da tsaki da su karfafa goyon bayan juna da tabbatar da hadin gwiwar kasa da kasa don dakilewa, da rage kaifi, da kuma kawo karshen annobar har ma da magance mummunan sakamakon da annobar ta haifar, sannan a kuma tabbatar da ba da kariya ga wadanda annobar ta fi shafa, da suka hada da mata, kananan yara, matasa, tsofaffi da masu bukata ta musamman, kana a dauki kwararan matakan yaki da labarun karya, da nuna kyama, da nuna wariyar launin fata da kuma nuna banbancin kasa ko shiyya.

Sanarwar hadin gwiwar ta kuma amince da bukatar a fara la’akari da rigakafin cutar COVID-19 a matsayin wani muhimmin kaya na al’ummar duniya don kyautata lafiyar al’umma. Haka zalika sanarwar ta yaba da gudunmawar da kasashe ke bayarwa wajen bullo da wasu tsare tsare don samar da rigakafin COVID-19 kamar shirin (ACT), da COVAX da makamantansu, domin bunkasa aikin samar da rigakafin da saukaka hanyoyin mallakarsu karkashin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa da kuma hadin gwiwar bangarori daban daban.(Ahmad)