logo

HAUSA

An gudanar da muhawara game da yaki da nuna wariyar launin fata a zaman kwamiti na 3 na babban taron MDD karo na 76

2021-10-01 15:57:31 CRI

A jiya Alhamis ne aka gudanar da muhawara, game da yaki da nuna wariyar launin fata, yayin zaman kwamiti na 3, na babban taron MDD karo na 76, karkashin hadin gwiwar jagorancin Sin da kasashen Afirka. Yayin mahawara wadda Najeriya ta jagoranta, an yi musayar yawu game da batutuwa da suka jibanci ayyukan kwamitin nazarin zamantakewar al’umma, da jin kai, da raya al’adu.

An kuma tattauna game da muzgunawar da wasu ‘yan sanda ke yiwa al’umma, da rashin daidaito tsakanin al’ummu, wanda hakan ya ja hankalin mahalarta zaman, game da bukatar gaggauta aiwatar da sanarwar bayan taron Durban, da manufofin yaki da nuna wariyar launin fata, da kyamar wasu rukunin al’ummu, da dai makamantan su.

Yayin da yake tsokaci gaban mahalarta taron, wakilin Najeriya ya ce, duk da cewa an shafe tsawon shekaru kusan 10 ana aiki tukuru, har yanzu akwai jan aiki a fannin yaki da wadannan matsaloli. Ya ce wadannan akidu sun bazu a sassan duniya, sun kuma haifar da kalubale, da muzgunawa ga dumbin mutane.

Ya ce al’ummu masu asali daga Afirka da Asiya, da wasu dake da tushe na asalin wasu kasashe, sun sha fama da nuna wariya, da kyama, da muzgunawa, kuma kawo yanzu ba a kai ga shawo kan tushen wannan matsala ba.

Jami’in ya kara da cewa, a yayin da ake fuskantar cutar numfashi ta COVID-19, wasu ‘yan siyasa da jagororin al’umma, sun rika yada jita hita da bayanan bogi, tare da kalaman batanci da na wariyar launi, wanda hakan ya kara ingiza nuna kyama ga wasu sassan al’umma.

Daga nan sai ya yi kira ga sassan kasa da kasa, da su dauki matakan wanzar da daidaito, da kare rayukan al’umma, da martaba hakkin wadanda suka taba fuskantar kangin bauta, da mulkin mallaka, musamman ma ‘yan kasashen Afirka.  (Saminu)