logo

HAUSA

Sin ta biya dukkan kudaden da ya kamata domin ayyukan wanzar da zaman lafiyar MDD

2021-10-01 16:15:49 CRI

Sin ta biya dukkan kudaden da ya kamata domin ayyukan wanzar da zaman lafiyar MDD_fororder_mdd

A ranar Alhamis kasar Sin ta biya dukkan kudaden da ya kamata ta biya domin gudanar da ayyukan shirin wanzar da zaman lafiya na MDD kimanin 12 da kwamitin sulhun MDD ya tsara, yayin da wa’adinsa zai cika a ranar 31 ga watan Disamba.

Sanarwar da tawagar kasar Sin dake MDD ta baiwa manema labarai, ta ce, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kuma mai wakilcin dindindin a kwamitin sulhun MDD, kana kasa ta biyu mafi bayar da gudunmawa ga kasafin kudin shirin wanzar da zaman lafiya na MDD, kasar Sin, a ko da yaushe tana biyan dukkan kudade da ya kamata ta biya ga MDD, kuma a kan lokaci, kuma cikakku, sannan ba tare da gindaya wasu sharruda ba.

Sanarwar ta kara da cewa, hakan ya kara bayyana yadda kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen tallafawa ayyukan MDD da manufar hadin gwiwar bangarori daban daban.

A bana ake bikin cika shekaru 50 da sake maido da halastacciyar kujerar wakilcin kasar Sin a MDD. Sama da shekaru 50 da suka gabata, kasar Sin a ko da yaushe ta kasance mai burin gina zaman lafiyar duniya, mai bayar da gudunmawar bunkasa ci gaban duniya, mai kiyaye dokokin kasa da kasa, kana mai samar da alherai ga bil adama, in ji sanarwar.(Ahmad)