logo

HAUSA

Kafar yada labaran Amurka: Amurka na jefa duniya cikin rikici

2021-09-30 16:49:42 CRI

Kafar yada labaran Amurka: Amurka na jefa duniya cikin rikici_fororder_美国-4

Sakatariyar baitil malin Amurka Janet L. Yellen, ta yi gargadi a ranar 28 ga wata cewa, idan har majalisar dokokin Amurka ta gaza warware batun  rikicin bashi mafi tsanani a kan lokaci, to akwai yiwuwar sashen baitil malin kasar zai shiga halin kamfar kudade ya zuwa ranar 18 ga watan Oktoba, kuma gwamnatin tarayyar kasar Amurka za ta fuskanci rikicin saba yarjejeniyar bashi na farko a tarihin kasar.

Damuwar da ake nunawa game da rikicin bashin Amurka ya haifar da rashin tabbas a kasuwannin hada hadar kudi na kasa da kasa a baya bayan nan. Wasu kafafen yada labaran Amurka sun yi tsokaci cewa, tasirin tsananin rikicin bashin Amurkan ya zarce iyakar Amurkar kadai, har ma yana neman jefa duniya cikin matsaloli.(Ahmad)