logo

HAUSA

Aljeriya ta fara samar da alluran rigakafin COVID-19 na Sinovac

2021-09-30 09:51:16 CRI

Aljeriya ta fara samar da alluran rigakafin COVID-19 na Sinovac_fororder_210930-yaya 1

Kasar Aljeriya ta fara samar da allurar rigakafin COVID-19 na kamfanin Sinovac na kasar Sin, karkashin wani hadin gwiwa tare da kasar Sin, a lardin Constantine na gabashin kasar.

An kaddamar da aikin samar da alluran ne a wani biki, wanda Firaministan Aljeriya Ayman Benabderrahmane da jakadan kasar Sin a Algeria Li Lianhe suka halarta, karkashin wani hadin gwiwar dake tsakanin kamfanin samar da magunguna na Sinovac Biotech na kasar Sin da kuma rukunin kamfanin samar da magunguna na Algeria wato Saidal.

A jawabinsa na bude bikin, Benabderrahmane ya ce, shirin samar da alluran, zai iya bude hanyar samar da wasu alluran rigakafi a nan gaba.

Ya kara da cewa, idan har aka samar da isasshen sinadaran hada alluran aka kuma samu oda daga cikin gida da sauran sassan kasa da kasa, shirin samar da alluran, zai samar da allurai miliyan 6 na allurar Sinovac zuwa karshen wannan shekarar, da allurai miliyan 96 kowace shekara bayan haka.

Tun bayan barkewar COVID-19, Aljeriya da kasar Sin, suke hadin gwiwa don yakar cutar. A watan Fabrairun shekarar 2020, Aljeriya na daya daga cikin kasashe na farko da suka aike da gudummawar kayayyakin kiwon lafiya zuwa kasar Sin, yayin da ita ma kasar Sin ta aike da tallafin kayayyakin kiwon lafiya da tawagogin likitoci da dama zuwa kasar ta Algeria. (Ibrahim)