logo

HAUSA

Jakadan Sin a Nijeriya ya halarci taron kwamitin gasar wasannin Olympics na Afirka

2021-09-30 10:53:16 CRI

Jakadan Sin a Nijeriya ya halarci taron kwamitin gasar wasannin Olympics na Afirka_fororder_hoto

Jiya Laraba, bisa gayyatar da aka yi masa, jakadan kasar Sin dake kasar Nijeriya Cui Jianchun ya halarci taron kwamitin zartaswa karo na 56 na kungiyar hadin gwiwar kwamitin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta kasashen Afirka, wanda aka yi a birnin Abuja, fadar mulkin kasar Nijeriya. A jawabinsa yayin taron, jakada Cui ya yi bayani game da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta yanayin sanyi da za a gudanar a birnin Beijing.

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasashen Afirka, Mustapha Berraf, da ministan harkokin matasa da wasanni na kasar Nijeriya, Sunday Dare, da wasu wakilan kasashen Afirka da na kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa, sun halarci taron.

A yayin taron, jakada Cui ya taya kasashen Afirka murnar nasarorin da suka cimma a gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta birnin Tokyo, ya ce, a shekarar 2022, kasar Sin za ta gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta yanayin sanyi, lamarin da ya sa, birnin Beijing zai kasance birni na farko, wanda ya taba karbar bakuncin gasar Olympics ta yanayin zafi da yanayin sanyi. Ya kuma nuna fatan cewa, ’yan wasan motsa jiki na kasashen Afirka, za su samu sakamako mai kyau yayin gasar wasannin Olympics ta yanayin sanyi da zai gudana a birnin Beijing.

A nasa bangare kuma, Mustapha Berraf ya taya kasar Sin murnar shirya gasar wasannin Olympics ta yanayin sanyi, ya ce, kasar Sin kasa ce mai samun ci gaba kan harkokin motsa jiki. Ya kara da cewa, A shekarar 2008, kasar Sin ta cimma nasarar shirya gasar wasannin Olympics ta yanayin zafi, kuma tabbas ne, a wannan karo ma, kasar Sin za ta cimma nasarar shirya gasar wasannin Olympics ta yanayin sanyi. (Maryam)