logo

HAUSA

’Yan sanda sun kama mambobi 42 na kungiyar Shi’a da aka haramta ayyukanta a Nijeriya

2021-09-29 09:46:14 CRI

Rundunar ’yan sandan Nijeriya, ta kama mambobi 42 na kungiyar mazhabar shi’a da aka haramta ayyukanta a kasar, yayin wani tattaki da ya rikide zuwa rikicin a Abuja, babban birnin kasar.

A cewar Josephine Adeh, kakakin rundunar ’yan sandan Abuja, ’yan kungiyar da suka fito daga jihohin arewacin kasar na Niger da Bauchi da Gombe da Borno da Kaduna, sun je birnin Abuja ne domin tada rikici.

A cikin watan Yulin 2019 ne Nigeriya ta ayyana kungiyar ta Shi’a a matsayin haramtacciya, tana mai cewa ayyukanta na barazana ga tsaron kasar da doka da oda da gudanar da harkokin addini da zamantakewa cikin lumana da kuma cikakken ’yancin kasar.  (Fa’iza Mustapha)