logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga da dama a yankin arewa maso yammacin Najeriya

2021-09-28 14:20:45 CRI

Rahotani daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram da ‘yan bindiga masu yawa a wani artabu da sojojin a wani sansanin soji da ke jihar Sokoto a yankin arewa maso yammacin kasar.

Mai magana da yawun hedkwatar tsaron kasar Benjamin Sawyer, ya bayyana cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai cewa, an kashe 'yan bindigar ne bayan da dakarun Operation Hadarin Daji suka dakile wani harin hadin gwiwa da ‘yan Boko Haram da 'yan bindiga suka yi yunkurin kaiwa a kwanan nan kan sansanin sojojin da ke Burkusuma, wani yanki mai nisa da kan iyaka.

Ya ce, yayin arangamar, an jikkata sojojin da bai bayyana adadinsu ba. Sai dai kuma, sojojin na ci gaba da farautar maharan. (Ibrahim)

Ibrahim