logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya za ta shawo kan kalubalen tsaro nan da watan Maris na shekarar 2022

2021-09-28 19:57:56 CRI

Shugaban kwamitin hadin gwiwa game da tsaro a majalissar wakilan Najeriya Babajimi Benson, ya ce gwamnatin Najeriya za ta shawo kan kalubalen tsaro dake addabar kasar nan da watan Maris na shekarar 2022.

Dan majalissar, wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da jaridar Vanguard cikin makon jiya, ya ce gwamnatin Najeriya ta umarci sassan rundunonin tsaron kasar, da su aiwatar da dukkanin matakan da suka wajaba, don ganin bayan ayyukan ‘yan bindiga, da sauran bata gari dake addabar al’ummar kasar, kafin watan Maris na shekarar dake tafe. (Saminu)