logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a kawar da makaman nukiliya daga duniya

2021-09-27 10:28:38 CRI

MDD ta yi kira da a kawar da makaman nukiliya daga duniya_fororder_0927UN chief-Fa'iza

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi jawabi albarkacin ranar kawar da makaman nukiliya ta duniya da ta fado a jiya Lahadi. Yana mai cewa dole ne a kawar da makaman nukiliya daga duniya, kana a bude sabon babi na tattaunawa da aminci da zaman lafiya.

A cewarsa, kawo karshen makaman nukiliya ya kasance aikin da MDD ta sa a gaba tun bayan kafuwarta.

Antonio Guterres ya ce kudurin zauren majalisar na farko a 1964, ya nemi kawar da makaman nukiliya da sauran makaman kare dangi.

Ya kara da cewa, duk da cewa adadin makaman nukiliya na ci gaba da raguwa cikin gomman shekarun da suka gabata, akwai tarin wasu 14,000 a fadin duniya, wadanda ke fuskantar barazana mafi muni cikin shekaru kusa 40 da suka gabata.  

Ya ce yanzu lokaci ya yi na kawo karshen wannan barazana da kawar da makaman daga doron duniya domin shiga wani sabon zamani na tattaunawa da aminci da zaman lafiya tsakanin jama’a. (Fa’iza Mustapha)