Dabarun Kasar Sin Sun Nuna Yadda Ta Sauke Nauyin Dake Bisa Wuyanta
2021-09-22 20:07:03 CRI
Ranar 21 ga wata, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya halarci babbar muhawara ta babban taron MDD karo na 76 ta kafar bidiyo daga nan Beijing, tare da gabatar da jawabi, inda ya bayyana wasu sabbin ra’ayoyi da matakai dangane da yaki da annobar COVID-19 cikin hadin gwiwa, farfado da tattalin arziki, raya hulda a tsakanin kasa da kasa da kyautata tafiyar da harkokin kasa da kasa. Ana ganin cewa, jawabin Xi ya nuna wa duniya alkibla, tare da karfafa gwiwar kasa da kasa da kara kuzari, jawabin da ya nuna jaruntakar kasar Sin da kuma yadda ta sauke nauyin dake bisa wuyanta.
Jawabin Xi ya ba da amsa kan fannoni guda 4 mafiya muhimmanci wadanda ya dace a gaggauta warware su a halin yanzu a duniya, wato wajibi ne a kawo karshen annobar COVID-19, wadda take shafar makomar dan Adam. Wajibi ne a farfado da tattalin arziki, a kokarin samun ci gaban duniya mai kyau ba tare da gurbata muhalli ba. Wajibi ne a kara hada kai, girmama juna, don samun nasara tare. Wajibi ne a kyautata tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa yadda ya kamata bisa ka’idar kasancewar sassa daban daban a duniya. Wadannan fannoni 4 sun bayyana burin kasashen duniya, musamman ma kasashe masu tasowa. Kuma kasar Sin ta fito da nata dabaru.
Sabbin ra’ayoyi da matakai da shugaba Xi Jinping ya sanar a yayin babban taron na MDD sun shaida cewa, har kullum kasar Sin na dukufa wajen shimfida zaman lafiya a duniya, tana ba da gudummowa wajen raya duniya, tana kuma kiyaye oda da dokar kasa da kasa, tare da samar da hajar da kowa zai yi amfani da ita a duniya, kuma tabbas ne za ta samar wa kasashen duniya sabon zarafi ta hanyar raya kanta. Wannan shi ne zabin da kasar Sin ta yi a tarihi, kana shi ne alkawarin da ta yi wa duniya, lamarin da ya nuna yadda ta sauke nauyin dake bisa wuyanta. (Tasallah Yuan)