logo

HAUSA

Musayar Al’adu Da Sin Na Da Matukar Muhimmanci, In Ji Wani Jami’in Afirka Ta Kudu

2021-09-20 16:46:46 CRI

Shugaban sashen sadarwa na babban gidan wasan kwaikwayon “Artscape” dake kasar Afirka ta Kudu Simone Heradien, ya ce kamata ya yi kasarsa da kasar Sin, su fadada musaya a fannonin al’adu daban daban, kasancewar hakan zai inganta fahimtar juna tsakanin al’ummun su.

Simone Heradien ya ce "Ta hanyar musayar al’adu ne muke iya kara fahimtar juna". Jami’in ya yi wannan tsokaci ne da yammacin ranar Asabar, yayin zantawa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua, jim kadan bayan kammala bikin nuna wasanni da gidan wasannin kwaikwayonsa ya shirya, albarkacin cika shekaru 50 da bude sa, da kuma bikin cika shekaru 50 da fara shirya bikin nuna fasahohin kade kade na matasa, wanda ke baiwa matasan Afirka ta Kudu damar nuna kwarewarsu a mataki na kwararru.

Shi ma da yake tsokaci game da hakan, ministan raya al’adu da wasanni na lardin yammacin Cape Mr. Anroux Marais, ya shaidawa wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, musayar al’adu da Sin muhimmin mataki ne da ke baiwa al’ummun kasashen biyu damar kara koyi da juna, da hadin kai mai haifar da juriya da fahimtar al’adun juna, tare da kara inganta zaman tare.  (Saminu)

Saminu