logo

HAUSA

Tsohon shugaban Algeria Abdelazizi Bouteflika ya rasu

2021-09-18 17:20:34 CRI

Tsohon shugaban Algeria Abdelazizi Bouteflika ya rasu_fororder_0bd162d9f2d3572c54daca2ad764412e63d0c388

Gidan talabijin na ENTV na Algeria, ya sanar da mutuwar tsohon shugaban kasar, Abdelaziz Bouteflika jiya Juma’a, bayan samun sanarwa daga fadar shugaban kasar.

Bouteflika wanda ya rasu yana da shekaru 84, ya kasance ministan harkokin wajen kasar ne a shekarar 1963.

Ya kuma shiga zaben shugaban kasar na shekarar 1999, inda ya samu gagarumar nasara.

Abdelaziz Bouteflika, ya kasance matsayin shugaban kasar tsawon wa’adi 4 a jere, har zuwa watan Afrilun 2019. (Fa’iza Mustapha)