logo

HAUSA

Tawagar ECOWAS ta tattauna da sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea

2021-09-18 17:22:04 CRI

Tawagar ECOWAS ta tattauna da sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea_fororder_8601a18b87d6277fbf667ddc72c33e39eb24fce6

Tawagar da ta kunshi manyan jami’an kungiyar ECOWAS mai raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ta tattauna da sojojin da suka yi juyin a Guinea, tare da ganawa da shugaban kasar Alpha Conde, wanda ke tsare.

Tawagar wadda ke karkashin shugaban ECOWAS na wannan karo kuma shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo da sauran mambobinta da suka hada da shugaban hukumar kungiyar Jean-Claude Kassi Brou da shugaban Cote d’ivore Allassane Ouattara, sun gana da shugaba Conde ne bayan ganawar sirri da suka yi da shugaban sojin, jiya Juma’a a Conakry, babban birnin kasar Guinea.

Daga bisani, Nana Akufo Addo ya ce sun gamsu da sakamakon tattaunawar. Inda shugaba Ouattara kuma ya ce, Alpha Conde na cikin koshin lafiya.

A ranar 5 ga wata ne aka yi juyin mulki a kasar, inda sojoji suka tsare shugaba Alpha Conde tare da rushe gwamnatinsa, kana suka ce za su kafa gwamnatin hadin kan kasa. (Fa’iza Mustapha)