logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Niger ya musanta karairayin da kasashen yamma ke yi game da Xinjiang a kafofin watsa labarai na kasar

2021-09-17 11:33:14 CRI

Jakadan Sin dake Niger:ya musanta karairayin da kasashen yamma ke yi game da Xinjiang a kafofin watsa labarai na kasar_fororder_微信图片_20210917092151

Jakadan Sin dake Niger Jiang Feng, ya gabatar da bayani mai taken “Ana bukatar kokari mai dorewa wajen yakar ta’addanci”, a kafar yada labarai ta ANP da sauran jaridun jamhuriyar Niger, da nufin musanta karyar da wasu kasashen yamma suka yi game da batun yankin Xinjiang, da fayyace hakikanin yanayin “kotun musamman kan harkokin Uygur”.

Bayanin ya bayyana cewa, yaki da ta’addanci mataki ne da ya wajaba kowacce kasa ta dauka. Ya ce Sin na mai da hankali sosai kan tsaron kasa, kuma tana iyakacin kokarin dakile duk wani aikin ta’addanci. A sa’i daya kuma, Sin na nuna himmantuwa wajen taka rawa ta fuskar yakar ta’addanci a duniya.

A cewarsa, ta’addanci kalubale ne da duk fadin duniya ke fuskanta, dole ne a kaucewa nuna fuska biyu kan wannan batu. Ya ce Sin tana kokarin bullo da hanyar da ta dace na yakar ta’addanci da kawar da tsatsauran ra’ayi bisa halin da kasar ke ciki. Kana tana fatan more dabara da fasaharta da kasashen waje don kara karfin hadin kai wajen yakar ta’addanci. (Amina Xu)