logo

HAUSA

UNICEF: rashin tsaro ya hana yara miliyan 1 komawa makaranta a Nijeriya

2021-09-17 10:21:22 CRI

UNICEF: rashin tsaro ya hana yara miliyan 1 komawa makaranta a Nijeriya_fororder_210917-fa'iza-1-makarantar Nigeriya

Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya ce yara a kalla miliyan 1 ne suka gaza komawa makaranta saboda fargabar rashin tsaro a sassa da dama na Nijeriya, yayin da a wasu sassan aka fara sabon zangon karatu a watan Satumba.

Sanarwar da asusun UNICEF ya fitar, ta ruwaito cewa, an katse wasu dalibai daga samun ilimi da sauran fa’idojin da ake samu daga makarantu, saboda fargabar da iyalai da al’umma ke yi na tura ’ya’yansu makaranta, biyo bayan shafe watanni da dama da aka yi ana kai jerin hare-haren kan makarantu da sace dalibai a Nijeriya.  (Fa’iza Mustapha)