ECOWAS za ta nemo matakai masu dorewa na warware rikicin siyasar Guinea
2021-09-17 09:57:15 CRI
Shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), sun fara gudanar da muhimmin taron koli a ranar Alhamis game da batun juyin mulkin sojoji a kasar Guinea.
Taron kolin shi ne karo na biyu da shugabannin kasashen 15 na shiyyar kudancin hamadar Afirka suka gudanar tun bayan yujin mulkin sojoji a ranar 5 ga watan Satumba.
Shugaban kungiyar ECOWAS, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya bayyana kwarin gwiwa cewa kungiyar za ta lalibo matakai masu dorewa na warware rikicin siyasar kasar Guinea. A yayin jawabin bude taron, Akufo-Addo ya ce, wadannan matakai suna da matukar muhimmanci wajen tabbatar da dorewar zaman lafiyar siyasa da kwanciyar hankali da kuma hadin kan shiyyar. (Ahmad)