logo

HAUSA

An yiwa mutanen da yawansu ya kai kimanin miliyan 1.6 allurar riga kafin COVID-19 a karo na biyu a Najeriya

2021-09-16 13:43:06 CRI

Jaridar Vangard ta Najeriya ta ba da labarin cewa, darektan hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasar Faisal Shuaib, ya ce zuwa ranar 13 ga wata, an yiwa mutane 1,692,315 allurar rigakafi karo na biyu, yayin da aka yi wa wasu 4,052,756 a karon farko.

Faisal Shuaib ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai da ya kira dangane da halin da ake ciki na yakar cutar COVID-19 a kasar, inda ya ce zuwa yanzu, gwamnatin Najeriya ta samu alluran riga kafi na kamfanin Modena 2,000,040, kuma daga cikinsu an riga an yi amfani da kashi 70.4%. Aa ce, yanzu jihohi daban-daban na Najeriya sun fi zabar allurar kamfanin AstraZeneca na Amurka, lamarin da ya sa aka nemi su yi amfani da allurar Modena da bai wuce 50% ba, don tabbatar da alluran sun isa a yi wa mutane a karo na biyu. (Amina Xu)