logo

HAUSA

Hauhawar farashin kayayyaki na kara raguwa a Najeriya

2021-09-15 20:49:06 CRI

Hauhawar farashin kayayyaki na kara raguwa a Najeriya_fororder_1133588817491918877

Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS, ta ce ya zuwa watan Agustan da ya gabata, kasar ta samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki cikin watanni 5 a jere, inda alkaluman awon sauyin tsadar kayayyaki da na hidimomi wato CPI, ya karu da kaso 17.01 bisa dari kwatankwacin makamancin lokacin bara, kamar dai yadda hakan ke kunshe cikin wasu alkaluma da hukumar ta NBS ta fitar a Larabar nan.  (Saminu)