logo

HAUSA

Kwamitin tuntubar kasar Guinea ya shafe wunin farko na taronsa

2021-09-15 14:57:23 CMG

Kwamitin tuntubar kasar Guinea ya shafe wunin farko na taronsa_fororder_11

Wakilin CGTN karkashin babban gidan radiyo da talabijin na kasar Sin, Desri Conon, ya bada rahoto a ranar 14 ga watan Satumba agogon kasar Guinea cewa, kwamitin tuntubar kasar Guinea ya kaddamar da fara taronsa na tsawon kwanaki hudu a dakin taro na "People's Palace" dake harabar ginin majalisar dokokin kasar a Conakry, babban birnin kasar Guinea.

Osman Kabbah, shugaban jam’iyyar Guinea Democratic Hope Party, ya ce bangarorin da abin ya shafa sun yi tattaunawa mai armashi. Wannan shi ne karon farko da jiga-jigan ‘yan siyasar kasar suka gana da gwamnatin sojin kasar, kuma sojojin sun bayyana kyakkyawar aniyar kafa gwamnatin rikon kwarya biyo bayan juyin mulkin kasar. Kabbah ya yi amanna cewa, wannan karon ya sha bambam da irin rikicin da aka samu wajen mika mulki a kasar Guinea a shekarun 2008 da 2009. A wannan karo dukkan bangarori za su yi aiki tare wajen kafa tarihin kulla yarjejeniyoyi da kafa sabbin hukumomin zabe mafiya dacewa da tsarin kasa da kasa. Dole ne dukkan bangarori su martaba yarjejeniyoyin kasar Guinea da kasa da kasa, musamman hadin gwiwarta da kasar Sin.(Ahmad)

Bello