logo

HAUSA

Shugaba Buhari na Najeriya ya nemi amincewar majalisar dattijai don karbo bashi daga ketare

2021-09-15 10:03:15 CMG

Shugaba Buhari na Najeriya ya nemi amincewar majalisar dattijai don karbo bashi daga ketare_fororder_1,jpg

Bayanan da jaridar Daily Trust ta Najeriya ta wallafa ya nuna cewa, shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya gabatar da wasika zuwa ga shugaban majalisar dattijan Najeriya Ahmad Lawan, inda yake neman amincewarta don baiwa gwamnatinsa damar karbo rancen dala biliyan 4, da Euro miliyan 710, a matsayin sabon rance daga ketare, da kuma kudin tallafi na dala miliyan 125, wanda zai karbo daga bankin duniya, da hukumar bunkasa cigaba ta Faransa, da bankin fici da shigi na Faransa, da kuma asusun bunkasa ayyukan noma na kasa da kasa.

Wasikar ta bayyana cewa shugaba Buhari, ya tattauna batun karbar sabon rancen kudaden na ketare tare da bangarorin da abin ya shafa, kuma gwamnatin tarayya tana son yin amfani da kudaden ne wajen gudanar da muhimman ayyukan more rayuwa a bangarori daban daban a duk fadin kasar.(Ahmad)

Ahmad