logo

HAUSA

Nijeriya ta kasance kasa ta biyu a Afirka da ta fi cinikayya da lardin Hunan na Sin

2021-09-15 10:56:11 CRI

Nijeriya ta kasance kasa ta biyu a Afirka da ta fi cinikayya da lardin Hunan na Sin_fororder_0915-01

Bisa alkaluman da hukumar kwastam ta birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin ta bayar a ranar 13 ga wata, tun daga watan Janairu zuwa Agustan bana, yawan kudin cinikin shige da ficen kayayyaki tsakanin lardin Hunan da nahiyar Afirka, ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 24.87, wanda ya karu da kashi 43.7 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara. Kasashen Afirka ta Kudu, da Nijeriya, da Masar sun kasance kasashe uku mafi cinikayya da lardin Hunan na Sin tsakanin kasashen Afirka.

Bayan kaddamar da bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka a lardin Hunan, an gina filin kirkire-kirkire na hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka a lardin Hunan, inda ake sa ran za a shigar da sabbin kamfanoni fiye da 200 a bana, kana yawan kudin cinikin shige da fice a bana zai kai Yuan biliyan 15. Kana yayin bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka karo na biyu da za a gudanar a ranar 26 ga wannan wata, za a tattauna ayyukan hadin gwiwa 385, wadanda za su lakume kudin da yawansu zai zarce dala biliyan 59.46.

Bisa kokarin da hukumar kwastam ta birnin Changsha ta yi, an kara saurin shigar da kayayyakin amfanin gona na Afirka zuwa kasar Sin, kana Sin ta samu damar fitar da busasshen barkono zuwa nahiyar Afirka a karo na farko, an kuma kammala mataki na farko na tantance naman ragon kasar Madagascar, da naman saniya na kasar Uganda, da kayayyakin teku na Nijeriya da sauransu. (Zainab)